Kungiyar Boko Haram ta sace sama da mutane 300 a Damasak


-Kungiyar HRW ta nemi shugaba Buhari ya dawo da mutane sama da 300 wanda Boko Haram ta sace a Damsak a 2014

– Kungiyar ta bayya cewa mutane sunji tsoro bayyana hakan ne saboda kungiyar

– Harda yar shekara 7 cikin wadanda aka sace

Yan Kungiyar Boko Haram

An gano cewa kungiyar Boko Haram ta sace sama da mutane 300 a daga garin Damasak wanda yake a cikin jihar Borno. Kungiyar HRW ne ta gano hakan bayan wani bincike.

An gano cewa mutanen wurin sunyi kokarin sanar da gwamnati halin da ake ciki amma sai suka ji tsoron matakin da gwamnatin zata dauka.

Wannan ya faru ne bayan da gwamnatin ta gaza wajen ceton yan mata sama da 276 wadanda aka sace daga makarantar chibok a shekarar 2014.

Inda wani jami’in karamar hukumar yake magana da yan jaridar AFP a ranar 31 ga watan Maris, ya bayyana cewa sama da yara 300 ne cikin sama da mutane 500 wanda yan kungiyar Boko haram suka sace daga Damasak.

A cewar jami’in, diyar shi yar shekara 7 tana cikin wadanda aka sace.

Yace ” Mun boye maganar ne kawai saboda tsoron gwamnati bayan kunyar data sha daga sace yan matan Chibok.

” Kowanne iyaye na jin tsoron suyi magana.

“Wasu da sukayi magana da wakilan mu na majalisar wakilai dana majalisar dattawa sai kawai sukayi shiru abun su.

“Sun shigo gari inda suka sace yara daga iyayen su. Wasu ma bai wuce a basu mama ba. Diyar ya’ya na yar shekara 16 harda ita. Wasu ma tsakanin shekaru 5 zuwa 16.

A cewar kungiyar HRW, Boko Karam ta kama Zanna Mobarti bayan data amshe garin Damasak inda ta kama yara sama da 300 ta tilasta kulle makarantar Firamare dake garin kuma ta sanya su dole suyi karatun Arabiyya.

Wannan na zuwa ne bayan da wani rahoto ya bayyana cewa sama da mutane 17,000 ne suka rasa rayukan su tun bayan da kungiyar Boko Haram ta fara ta’addanci shekara 6 data wuce.Source link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *